Condoleeza Rice ta gana da ministoci 8 na kasashen larabawa
December 1, 2006Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice ta gana da ministocin harkokin wajen kasashen larabawa guda 8 kafin babban taronsu da zasu gudanar nan gaba,akan halin da ake ciki a yankin Paladinawa,Iraqi da kuma Lebanon.
Ministocin na larabawa sun jaddada bukatar dake akwai ta magance matsaylar yankin Paladinawa wadda itace ummul abaisin duk wani rikici a yankin gabas ta tsakiya tare da baiyana goyon bayansu ga shugaba Mahmud Abbas ,sun kuma mika goyon bayansu gwamnatin kasar Lebanon a kokarinta na sake gina kasar.
Kasashen sun hada da Jordan da Masar da kasashe 6 na majalisar hadin kai ta yankin Gulf.
Tun farko a jiya lahamis rice ta kai ziyara yankin Palasdinawa da na Israila inda ta tattauna da shugaba Mahmud Abbas da kuma firaminista Ehud Olmert,kann yiwuwar komawa tattaunawar zaman lafiya.