COP23: An fara taro kan sauyin yanayi a birnin Bonn
November 6, 2017![COP23 UN Klimakonferenz in Bonn](https://static.dw.com/image/41250116_800.webp)
Talla
Taron wanda za a dauki kwanaki 12 ana yi, na da wakilai dubu 25 ne daga sassa daban-daban. Kasashe 196 ke da wakilci lokacin taron na birnin Bonn. A bara ne dai kasashe suka hadu a birnin Paris na kasar inda suka cimma yarjejeniyar daukar kwararan matakan maganta bazanar sauyin yanayin da aka hakikance cewa manyan masana'antu na zamani na daga ciki.