1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yar fafutikar kare muhalli ta zargi kasashe da karya

Abdoulaye Mamane Amadou
December 11, 2019

Matashiyar nan 'yar fafutikar kare muhalli Greta Thunberg ta zargi manyan kasashen duniya da sharara karya game da alkawulan da suka dauka kan batun yaki da gurbatar muhalli.

Madrid Cop25 Greta Thunberg
Hoto: Imago Images/Agencia EFE/J.J. Guillen

Matashiyar ta ce kwarorin manyan kasashen duniya kalilan ne kawai masu karfin tattalin arziki suka aminta da rage fitar da iskar gaz da ke gurbata yanayi, kana kuma duk da yake yunkurinsu ya kasance abin armashi ga jama'a tun daga farko, daga bisani kasashen sun kasa cika wadannan alkawualan kamar yadda ya kamata, tana mai bayyana hakan a matsayin karya da yaudara in ji matashiyar.

Greta Thunberg na zargin matakan da kasashen suka dauka kan batun rage dimamar yanayi, ba su shafi wasu fannoni ba, musamman ma jiragen sama da na jiragen ruwa, baya ga fannonin shige da ficen kayayaki.