Masar ta bude taron duniya kan sauyin yanayi
November 6, 2022Talla
An bude babban taron MDD kan sauyin yanayi da aka yi wa lakabi da COP27 a kasar Masar. Wannan taro shi ne karo na farko tun bayan da rikicin Rasha da Ukraine ya sauya duniya.
A yayin jawabinsa na mika ragamar COP27 daga hannun Birtaniya zuwa kasar Masar, shugaban da ya jagorancin taron sauyin yanayin da ya wuce a Birtaniya Alok Sharma, ya ce wajibi ne shugabannin duniya su tashi tsaye domin tunkarar kalubalen sauyin yanayin da ke kara bunkasa a doron kasa. Taron dai zai gudana ne daga wannan Lahadi zuwa ranar Jumma'a 18 ga watan Nuwamba.