1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

COP28: Masana sun bukaci tallafawa kasashe masu tasowa

December 12, 2023

COP28: Masana sun ce akwai bukatar a tanadar da biliyoyin daloli wajen tunkarar kalubalen sauyin yanayi ta hanyar samar da bishiyu a kasashe mataluta.

Hoto: Peter Dejong/AP Photo/picture alliance

 

Gabanin kammala taron sauyin yanayi na duniya a Dubai dake Hadaddiyar Daular Larabawa, an cimma matsayar cewa akwai bukatar a tanadar da biliyoyin daloli wajen tunkarar kalubalen sauyin yanayi ta hanyar samar da bishiyu a kasashe masu tasowa.

Masana sun ce idan har ana son fitar da kasashe masu tasowa daga kalubalen sauyin yanayi dole ne a kashe makuden kudade ta hanyar samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da makamashin sola da dasa bishiyoyi a kasashen harma da samar da makamashi ta hanyar amfani da hasken rana, domin rage gurbatar yanayi ta amfani da iskar gas da kwal da kuma fetur dake gaba-gaba a gurbata muhalli.

A bara dai an ware kimanin dala triliyan daya da rabi domin tunkarar wannan kalubale, kamar yadda shugaban kamfanin dake kula da sauyain yanayi na Global Carbon , Yousef Alhorr, ya ce wadannan makuden kudade ne da kasashen ke bukatar su yi karatun ta nutsu, wajen bujiro da sabbin tsare-tsaren da zasu taimakawa kasashensu domin tunkarar kalubalen sauyin yanayi.

Masu fada a ji kan  batun sauyin yanayi da suka hadar da tsohon sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da hukumomi irinsu Bankin Duniya da ma Majalisar Dinkin Duniya tun da fari dai sun bukaci samar da daidaito a kasuwannin makamashi a duniya, tare da sa ido wajen tabbatar da tattara kudade ga kasashe masu tasowa.