COP29: An ware wa kasashe matalauta kudin diyya
November 24, 2024Yarjejeniyar karshe da aka cimma a babban taron alkinta muhalli na duniya da ya gudana a Baku na kasar Azerbaijan, ya kai ga amincewa da rika bai wa kasashe masu raunin tattalin arziki da gurbatar muhalli ya yi wa illa tallafin dala biliyan 300 a duk shekara.
Karin bayani : Yadda Afirka da wasu sassan duniya ke fama da karancin ruwan sha
Sai dai kuma kudin da aka amince a yayin taron sauyin yanayi na duniya na bana wato COP29 da ya gudana a Azerbaijan, bai kai kusa da adadin kudaden da kasashe masu tasowa suka bukata ba. Duk da kwashe tsawon mako biyu ana kai ruwa rana game da batun a taron, wakilan manyan kasashen sun ce wannan yarjejeniyar tana kan daidai, tare da fatan samar da karin wasu kudi nan gaba. Ko da yake masu wakiltar kasashen masu karamin karfi sun fice daga zauren taron na sauyin yanayi.
Karin bayani : Rage amfani da makamashin da ba a sabuntawa
Ana kyautata fatan wannan sabon kunshin tallafi zai taimakawa kasashen wajen daidaita matsalar dumamar yanayida kuma diyya ga irin barnar da sauyin yanayi ya haddasa musu.