1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

COP29: Kalubalen sauyin yanayi na duniya

Mouhamadou Awal Balarabe
November 11, 2024

Duk da cewar shugabannin manyan kasashen da ke gurbata iskar muhalli wato Chaina da Amurka ba za su halarta ba, amma batun samar wa kasashe masu tasowa kudaden yaki da ambaliya da fari da guguwa na haifar da muhawara,

Aserbaidschan BAKU UN Klimakonferenz COP29
Hoto: Alexander Nemenov/AFP

Kungiyoyi masu zaman kansu da dama sun soki lamirin shirya COP29 a Azerbaijan, saboda gwamnatin kasar na daukar arzikinta na man fetur a matsayin "kyauta daga Allah", a daidai lokacin da ake neman rungumar makamashin da ba ya gurbata muhalli. Dama, hukumomin kasar sun yi kaurin suna a fannin kama masu fafutukar kare muhalli tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

Babbar ajandar da taron na COP29 ya sa a gaba shi ne tsara adaddin tallafin da kasashen da suka ci gaba za su bai wa kasashe masu tasowa domin su fuskanci matsalar karuwar zafi da kuma ta ambaliya ruwa, tare da karfafa musu gwiwa su daina amfani da kwal ko man fetur domin samun bunkasar arziki. Ko da shi ke dai a shekara ta 2022, an kayyade musu dala biliyan 116 a kowace shekara, amma kasashe matalauta na bukatar alkawari na biliyoyin daloli a shekara.

Karin Bayani:Shugaban Brazil ya nemi duniya ta magance sauyin yanayi

Hoto: Sean Gallup/Getty Images

Sai dai kasashen yammacin duniya na ganin wannan tsari a matsayin abin da ba zai iya yiwuwa ba, duba da matsalolin da suke fama da su.

Saifullah Khan Dilazak, wakilin Pakistan ya ce sabanin ra'ayi da ake fuskanta kan hanyoyin magance sauyin yanayi, ba zai hana cimma matsaya ta bai daya ba:

"Ina matukar fatan ganin mun samu cimma wasu shawarwari da za su amfani wadanda za a haifa nan gaba, kuma a cimma muradin kare ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2030 da kuma mutunta yarjejeniyar Paris."

Karin Bayani: Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan yawan ta'adin zafi

Sai dai, barazanar da ke zuwa daga zababben shugaban Amurka Donald Trump na sake bin sahun Iran da Yemen da Libiya na fita daga yarjejeniyar da aka kulla a birnin Paris a shekarar 2015 na haddasa fargaba kan makomar yaki da dumamar yanayi a duniya. Kididdiga ta nunar da cewar wannan yarjejeniya ta ba da damar inganta halin dumamar yanayi a cikin shekaru goma da suka gabata zuwa kusan maki 3° a ma'aunin Celcius. Sai dai kwararru sun yi kira da a ci gaba da kokarin sauke dumamar yanayi zuwa maki 1.5° a ma'aunin Celcius, domin a magance matsalar ambaliya da aka yi fama da ita a yankuna da dama na duniya a 2024.

Karin Bayani: Nahiyar Asiya da Iftila'in sauyin yanayi

Hoto: Sergei Grits/AP Photo/picture alliance

Otávio Oscar Nunes do Nascimento, wakilin Brazil a COP29, ya nuna kaduwa game da barazanar da yarjejeniyar sauyin yanayi ke fuskanta daga Amurka:

"Muna cikin fargaba game da hakan saboda muna bukatar hadin gwiwa na duniya don yakar sauyin yanayi. Yanzu idan ba a yi yakin tare da Amurka ba, wacce ke da girma kuma ke da muhimmanci, ina tsammanin wannan yarjejeniyar ta duniya za ta yi rauni idan ta fice."

Kasashe Turai da dama sun yi alkawarin rubanya kokarinsu don cike gibi a fannin yaki da sauyin yanayi idan Amurka ta janye daga yarjejniyar Paris. Amma wasu daga cikin manyan shugabanninta irin su Emmanuel Macron na Faransa ko shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ba za su halarci taron kolin na shugabannin kusan100 a ranakun Talata da Laraba ba. Hasali ma dai, kalilan daga cikin shugabannin kungiyar G20 ne za su halarci taron. Shi ma  Lula na kasar Brazil ba zai halarta ba, duk da cewar kasar ce za ta karbi bakuncin COP30 a shekara mai zuwa.

Karin Bayani:Rage amfani da makamashin da ba a sabuntawa

Hoto: Jakub Porzycki/NurPhoto/picture alliance

Rodrigo Andrade, da ke wakiltar kasar Chile a taron COP29 ya yi fatan ganin kasashe masu hannu da shuni sun taimaki kasashe 'yan rabbana ka wadata mu wajen magance matsalolin da ke addabarsu:

"Kasar Chile ta na fama da bala'in fari mai tsananin gaske, don haka zan so in koma gida da tallafin fasaha da kudade don yaki da fari, saboda noma na bukatarsa."

 Kimanin mahalarta 51,000 ne suka hallara a Baku, a cewar hukumar kula da yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya, adadin da ya yi kasa idan aka kwatanta da COP28 da ya gudana a Dubai a bara.