1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
YanayiJamus

Jamus za ta tallafa a yaki sare dazuzzuka

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 7, 2025

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya yi kira da a samu hadin kan duniya domin yakar sauyi ko dumamar yanayi, tare da yin alkawarin samar da karin tallafin kudin da za yi amfani da su wajen kare dazuzzuka.

Brazil | Taro | Sauyin Yanayi | COP30 | Tallafi | Kudi | Jamus | Friedrich Merz
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich MerzHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Shugaban gwamnatin Jamus din Friedrich Merz ya yi wannan kiran ne, yayin taron sauyi ko dumamar yanayi na COP30 da ke gudana a yanzu haka a kasar Brazil.

A cewarsa Jamus za bayar da kudi masu kauri, domin zubawa a asusun da aka tanada na biliyoyin kudi da nufin yakar sare dazuzzuka a kasashe kamar Brazil da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

Karkashin wata shawara da Brazil ta bayar, kasashe mawadata za su samar da dalar Amurka biliyan 25 ga asusun da aka kiyasta kimanin kasashe masu tasowa 70 da ke da dazuzzuka za su amfana da shi.