1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chaina ta bude kofofinta bayan corona

March 14, 2023

Chaina za ta fara bayar da tarkardar izinin shiga kasarta wato visa, bayan shekaru uku da daukar tsauraran matakai na rufe kofofinta sakamakon annobar coronavirus.

China | Xi Jinping
Hoto: GREG BAKER/AFP

Cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Chainan ta fitar ta ce, kasar za ta fara bayar da ko wacce irin visa har ma da ta zuwa yawon buda ido. Sanarwar ta kara da cewa duk wata visa da aka bayar kafin rufe kofofin kasar a ranar 28 ga watan Maris na 2020, za ta ci gaba da aiki. Matakin na zuwa ne 'yan kwanaki kalilan bayan da majalisar kasar ta sake bai wa shugaba Xi Jinping sabon wa'adin mulki na shekara biyar, kuma a yayin da kasar ke laluben hanyoyin sake farfado da tattalin arzikinta da ya fada garari sakamakon annobar ta corona.