Karancin abinci na tunkarar duniya saboda Corona
April 1, 2020![Afrika Reis](https://static.dw.com/image/51588216_800.webp)
Talla
Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar da ke kula da kasuwanci ta duniya, WTO ne suka sanar da wannan gargadi. Hukumomin sun ce dokar kulle da gwamnatoci a duniya suka sanya tayi mummunar takaita hada-hadar kayan abinci a kasuwannin duniya.
Kazalika sun ce a kasashe da dama na duniya jama'a sun yi rige-rigen sayen kayan abinci kafin a sanya musu dokar hana fita saboda annobar Coronavirus, abin da ya kara haifar da karanci da tsadar abinci a wasu wurare. A don haka Majalisar Dinkin Duniya ta ce dole ne kasashe su rika barin sukunin yin safarar kayan abinci a kokarinsu na sanya dokar kulle don takaita Coronavirus.