1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yadda tasirin corona ya shafi tattalin arzikin Najeriya

March 19, 2020

A  cigaba da fuskantar tasirin annobar Coronavirus ga tattalin arzikin tarrayar Najeriya gwamnatin kasar ta ce za ta zaftare kaso 15 cikin dari na kasafin kudin kasar na Trilliyan 10 da ta tsara kashewa a bana.

Nigeria Kabinett Muhammadu Buhari Präsident
Hoto: Reuters/A.Sotunde

Duk da cewar dai annobar ta Coronavirus na kara bayyana tsakanin al'ummar tarrayar Najeriya, tasirinta a harkokin rayuwa na zaman kan gaba cikin radadin da ke neman dakile harkokin tattalin arzikin kasar wanda hakan ya sa gwamnatin ta ce za ta rage akalla kaso 15 cikin dari na kasafin kudin kasar sakamakon rashin kudin shiga da ya zama ruwan dare saboda annobar coronavirus.

Naira trilliyan daya da miliyan dubu dari biyar na kudaden da aka tsara za su kasance kudaden harkokin yau dana gobe ne dai a cewar ministar kudin kasar Zainab Ahmed,  gwamnatin ke shirin za ta zaftare daga kasafin

Bututan matatar mai ta NajeriyaHoto: picture-alliance/A. Holt

Har ya zuwa ranar yau dai farashin man fetur na kusan dalar Amruka 30 kasa da abun da kasar ta yi kasafi kansa a shekarar bana. To sai dai kuma ko bayan masana'antar man da ta kai ga ragin farashin man fetur din a tsakanin al'umma, harkar sufurin sama na zaman daya a cikin wadanda suke ji a jiki inda kuma asarar ke zaman ta daruruwan miliyoyin daloli.

Fadar gwamnatin ta ce za ta rufe tashoshin jiragen sama da ke biranen Kano da Fatakwal da kuma Enugu ko bayan haramta zirga zirga ga wasu kasashe 13 a filayen jiragen Legas da Abuja a fadar ministan sufurin sama na kasar Hadi Sirika.

Tarrayar Najeriyar dai na cikin siradi mai wahala ga kasar da fito cikin masassarar tattalin arziki shekaru hudu da suka wuce sannan kuma ke fuskantar sabuwar barazanar sake komawa.