Shugabanin kasashen Turai na karfafa matakan yakar corona
October 29, 2020Faransa ta aiyana dokar kulle a karo na biyu tun bayan bullar annobar corona, a kokarinta na shawo kan cutar da ke ci gaba da yaduwa kamar wutar daji a kasar. Shugaba Emmanuel Macron ya sanar da daukar matakin a daren jiya Laraba a jawabin da ya gabatar ma 'yan kasa ta kafar talabijin.
Yaduwar cutar, batu ne da ya zo mana da mamaki inji Shugaba Macron a yayin gabatar da jawabinsa. A Jamus kuwa, mahukunta sun amince da a rufe duk gidajen sayar da abinci da gidajen kallo a dokar da za ta soma aiki daga ranar biyu ga watan Nuwamba mai zuwa.
A kasar Indiya kuwa, mutum fiye da miliyan takwas cutar ta kama kamar yadda alkaluma suka nunar a wannan Alhamis, baki daya cutar ta kama mutum sama da miliyan arba'in da hudu, mutum miliyan daya da dari biyu ta hallaka tun bayan bullarta a Disambar bara. A dai wani lokaci a wannan Alhamis, shugabanin kasashen Turai za su gana ta bidiyo don duba sabbin matakan daikile annobar da kawo yanzu ta salwantar da rayuka tare da gurgunta tattalin arzikin duniya.