Jamus za ta sake nazarin dokar kulle
November 16, 2020Talla
Shugabar gwamnatin Jamus Angele Merkel za ta sake ganawa da masu ruwa da tsaki na jihohin kasar 16 a wannan Litinin domin tattauna matsaya da tasirin kwarya-kwaryar dokar kullen da kasar ta sa a baya-bayannan.
Rahotanni na cewa an samu karuwar adadin masu kamuwa da cutar bayan sanya kwarya-kwaryar dokar kullen da ta shafi rufe gidajen abinci da barasa, yayin da gidajen tarihi da makaratu da wuraren ibada suka kasance a bude. Sai dai dubban 'yan kasar sun yi zanga-zangar adawa da dokar.