Jamus ta tanadin kayan gwajin mutum 500,000
March 26, 2020Talla
Christian Drosten babban jami'i da ke jagorantar cibiyar nazarin cututtuka nau'in Virus da ke birnin Berlin shi ne ya bayar da wannan tabbaci.
Masanin ya ce kokarin yin gwaji da Jamus ke yi shi ne yasa duk da cewa kasar tana ci gaba da samun karuwar masu Corona amma kuma cutar ba ta yin kisa sosai idan an kwatanta da sauran kasashe. Kawo yanzu dai mutane 37,300 ke dauke da Coronavirus din a cikin Jamus.
Wannan labarin na zuwa ne a daidai lokacin da a safiyar Alhamis din nan wani bincike ya nuna cewa akasarin Jamusawa sun nuna gamsuwa a kan yadda gwamantin Angela Merkel ke daukar matakan dakile yaduwar cutar Corona a kasar.