1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Tallafin biliyoyin Euro ga kamfanoni da jama'a

Mohammad Nasiru Awal MAB
March 25, 2020

Daga cikin matakan tallafin har da batun karin kasafin kudi na sama da Euro miliyan dubu 156 da za a yi amfani da su wajen biyan sabbin basussuka.

Ministan kudin Jamus Olaf Scholz a taron manema labarai kan tallafin kudi
Ministan kudin Jamus Olaf Scholz a taron manema labarai kan tallafin kudiHoto: dpa

A wannan Laraba majalisar dokokin Jamus ta Bundestag za ta yanke shawara kan tallafin gaggawa na dubban miliyoyin Euro ga kamfanoni da al'umma a dangane da annobar cutar Corona, kamar yadda ministan kudi Olaf Scholz ya yi bayani.

Daga cikin matakan tallafin har da batun karin kasafin kudi na sama da Euro  miliyan dubu 156 da za a yi amfani da su wajen biyan sabbin basussuka. Ciki akwai asusun daidaita al'amura da zai ba wa kasa damar shiga aikin tallafa wa kamfanoni da ba da garanti ga kamfanoni.

Da haka za a tallafa wa kasuwar hada-hadar hannayen jari da kudi. Budu da kari za kuma a taimaka wa bankin raya kasa na KfW da Euro miliyan dubu 600.