Corona: Mutane sun yi zanga-zanga a Jamus
September 12, 2020Talla
Gabannin gudanar da zanga-zangar, hukumomi sun sanar da hanata amma daga bisani wata kotu da sanyin safiyar ranar Asabar (12.09.2020) ta sahale musu kan su gudanar da zanga-zangar.
Guda daga cikin wadanda suka hallarci zanga-zangar ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA cewar sun fito don nuna rashin amincewar da matakan da ake dauka kan annobar da ya ce sam babu ita, inda ya ke cewar gwamati na amfani da annobar wajen barnatar da kudaden al'umma da kuma tauye musu hakki.
A share guda kuma, a wani bagaren na birnin na Munich wasu mutane wanda galibinsu matasa ne da kuma 'yan kungiyoyin kwadago sun gudanar da wani gangami na yin Allah wadai da masu adawa da matakan da hukumomi ke dauka na dakile bazuwar cutar ta corona.