1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona ta kashe mutane fiye da 2,000 a Amirka

Abdoulaye Mamane Amadou
April 11, 2020

Yayin da mutane fiye da 2,000 suka mutu a Amirka cikin sa'oi 24, adadin wadanda suka mutu da cutar covid-19 a fadin duniya sun haura mutum dubu 103 sakamakon kamuwa da cutar a kasashe 193.

USA | Coronavirus: Krankenhaus in New York
Hoto: Imago Images/ZUMA Wire/M. J. Lugo

Kididdigar ta ce ko baya ga mamatan cutar ta kuma kama mutane fiye da miliyan daya da dubu dari bakwai a daukacin kasashe 193 da suka bayyana samun bullar cutar.

A yanzu kasar Italiya, ita ce ke kan gaba a jerin kasashen da suka fi samun mace mace sakamakon cutar ta Covid-19, inda kididdigar kamfanin dillancin labarai na AFP ya nuna ta rasa 'yan kasarta kimanin mutum dubu 18, 849. sannan sai kasar Amirka wacce ya zuwa yanzu mamatantan suka kai dubu 18, 777 haka nan sai kuma kasar Birtaniya da ke da adadin mutanen da suka mutu kimanin dubu 8, 958 duk da yake a kasar Spain, kusan kwanaki uku a jere an sami raguwar adadin mamata a sakamakon cutar ta COVID 19.

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO ko OMS ta yi gargadi ga kasashen duniya da kadda su yi gaggawar dage dokar takaita zirga zirgar jama'a da suka yi, inda ta ce yin hakan na iya kara dagula al'amurra musamman kara yawan wadanda za su kamu da cutar.