Corona ta haddasa tauye 'yancin yan jarida
April 21, 2020Kungiyar kare hakkin 'yan jarida ta kasa da kasa Reporters Sans Frontieres ta bayyana cewa matsalar tauyen 'yancin aikin jarida za ta karu a duniya a shekaru 10 masu zuwa sakamakon yadda annobar Coronavirus za ta haddasa matsaloli tattalin arziki da rigingimun siyasa ga kasashe da kuma kara girman zaman doya da man ja da ake yi tsakanin 'yan jarida da gwamnatoci a wasu kasashen duniya.
Kungiyar ta Reporters Sans Frontieres ta bakin babban sakatarenta Christope Deloire ta bayyana damuwarta kan yadda wasu kasashen wadanda dama suka yi kaurin suna wajen tauye 'yancin aikin jarida suke fakewa a yau da wannan annoba wajen daukar matakan da ba za su iya dauka ba idan ana zaune lami lafiya wajen kuntatawa 'yan jarida da ma sauran al'umma.
Kungiyar ta ba da misalin kasashen Chaina da Iran wadanda suka fake da annobar ta Corona wajen daukar matakan toshe wasu kafofin yada labarai a yayin da kasar Hungary ta tanadi dokar hukuncin zaman kaso na shekaru biyar ga wanda ya yada labaran karya kan annobar.