Mahukuntan Chaina sun garkame wasu birane
February 1, 2020
Jami'an lafiya a Hubei yankin da yafi kowanne a kasar Chaina fuskantar cutar Corona sun bayyana cewar a yanzu akwai mutane dubu 7,153 wadanda ke fama da cutar a birnin mai dauke da al'umma kusan miliyan 11. Munin al'amarin dai ya sanya mahukuntan Chaina garkame wasu manyan biranen kasar.
Tuni Hukumar Lafiya ta duniya ta ayyana dokar ta baci kan cutar ta Corona mai saurin halaka wanda ya kamu. Kasashe da dama da suka hada da Amirka da Japan da Koriya ta Kudu da Birtaniya da kuma tarayyar Jamus sun kwashe al'ummarsu da ke zaune a kasar ta Chaina a wani mataki na kandagarki, yayin da wasu kasashen suka zabi takaita shigar matafiya daga Chaina. Ita kuwa kasar Rasha sanar da shirinta ta yi na rufe iyakoki tsakaninta da Chaina har sai al'amura sun daidaita.