Corona na cigaba da yaduwa a Turai
October 13, 2020A ranar Talatar nan ce, gwamnatocin kasashen kungiyar Tarayyar Turai suka kara tsaurara matakan yaki da annobar Corona, duba da yadda ake kara samun masu kamuwa da cutar. Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce kimanin mutane 700,000 ne aka samu dauke da cutar a makon daya gabata.
Kasashen Birtaniya da Faransa da Rasha da kuma Spaniya su ne ke da rabin yawan wadanda suka kamu a fadin nahiyar Turai. Sakamakon kara yawan gwajin cutar da ake yi, likitoci sun gargadi al'umma dangane da kara samun matasa masu karancin shekaru da ke kamuwa da cutar wanda hakan ka iya saka magabatansu cikin hadarin kamuwa da ita.
A baya bayan nan Firaministan Italiya Giuseppe Conte ya sanya dokar hana wasu wasanni da ma taron da ya wuce mutane wadanda ba 'yan gida daya da suka wuce mutum shida.