1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rufe gidajan barasa a Los Angeles

Abdourahamane Hassane
November 25, 2020

Annobar Corona na dada karuwa a Amirka a yayin da a kasashen Turai ake kokarin yin sassauci ga matakan kulle da aka tanada.

USA Los Angeles Thanksgiving Heimreise
Hoto: Lucy Nicholson/REUTERS

A Los Angeles hukumomin sun rufe gidajan sayar da barasa da gidajan sayar da abinci  har tsawon makonni uku daf da lokacin da ake shirin yin bukukuwan karshen shekara. Mutane dubu 260 suka mutu da cutar a Amirka kawo yanzu daga cikinsu dubu 20 a baya-baya nan. A halin da ake ciki  Faransa da Jamus na shirin yin sassauci ga matakan kule kafin nan da tsakiyar watan Disamba sakamakon yadda cutar ta corona ta fara raguwa.