1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona ta shiga Majalisar Dokokin Botswana

April 9, 2020

Shugaban kasa da 'yan majalisar kasar Botswana za su kebe kansu daga jama'a.

Botswana Vize-Präsident Mokgweetsi Masisi
Hoto: Imago/Xinhua

Wannan ya biyo bayan mu'amulla da suka yi da wata jami'ar kiwon lafiya wace a wannan Alhamis aka gano cewa tana dauke da Coronavirus.

A yayin da yake jawabi a gaban majalisar dokokin kasar, ministan lafiyar kasar, ya ce yana sanar da duk dan majalisar da ke wurin cewa wajibi ne daga wurin su kama hanya zuwa wurin kebe kansu. A ranar Laraba ce dai 'yan majalisar da shugaban kasar ta Botswana suka hadu a zauren majalisar kuma suka yi mu'amulla da ita wannan mai Coronavirus.


Wannan shi ne karo na biyu da Shugaban Kasar Mokgweetsi Masisi ta Botswana zai kebe kansa. A watan da ya gabata ya yi makonni biyu a kebe bayan da aka yi zullumin ya yi mu'amulla da mai Coronavirus.