1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona ta cika shekara daya da bulla a duniya

Mouhamadou Awal Balarabe AMA
March 11, 2021

Duk da cewa ba ta yi wa nahiyar Afirka rauni sosai kamar yadda aka yi hasashe tun da farko ba, cutar corona da ke cika shekara daya da bulluwa ta haifar da durkushewar tattalin arziki da gibi tsakanin al'umma.

Coronavirus | Brasilien auf dem Höhepunkt der Pandemie
Hoto: Eraldo Peres/AP/dpa/picture alliance

­­­Lokacin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta ba da sanarwar yaduwar kwayar cutar Covid-19 a duniya a ranar 11 ga Maris 2020, mutane 47 ne kawai suka kamu da ita a nahiyar Afirka, kuma babu ko mutum daya da ta kashe. Sai dai labarin ya fara shan bamban a halin yanzu, domin kuwa Hukumar Kula da Yaduwar Cututtuka ta Afirka (Afirka CDC) ta ba da rahoton cewa kusan mutane miliyan hudu ne aka tabbatar da cewa sun kamu da cutar, sannan ta lamshe rayukan fiye da mutune 106,000 ya zuwa ranar 9 ga Maris 2021.

Karin Bayani: Matsalar kin zuwa gwajin corona

Mummunan sakamako da annobar corona za ta haddasa a Afirka na dogon lokaci, sun hada da na tattalin arziki. Hasali ma kasashen wannan nahiya sun sha wahala matuka wajen musayar kasuwanci da durkushewar bukatun saye da sayarwa na duniya. Alal misali, rufe kan iyakoki ya kasance koma-baya ga yawon shakatawa a gare su. Cikin wata kididdigar wucin gadi da ya fitar, Bankin Duniya, ya ce tattalin arzikin kasashen da ke yankin kudu da hamadar Sahara ya ragu da kashi 3.7 a shekarar 2020. Ita ma kungiyar agaji ta Oxfam ta yi hasashen cewa cutar corona za ta kawo nakasu a yaki da talauci da ake yi a wasu yankuna na Afirka. Anja Osterhaus, manajar shirye-shirye na Oxfam a Jamus ta bayyana cewa "Wani rahoton kungiyar Oxfam a shekarar da ta gabata ya nuna cewa matsalar tattalin arziki da cutar ta corona ke haifarwa na iya sanya koma bayan shekaru 30 a yaki da talauci a wasu yankuna na Afirka. Wannan hasashe ya nuna cewar za a samu raguwar kashi 20 cikin 100 na kudaden shiga, ma'ana sama da mutane miliyan 400 za su fada cikin talauci, inda za su rika samun kasa da $ 1.90 a rana." 

Karin Bayani: Sama da fadi da kudin COVID-19 a Afirka

Hoto: Fatemeh Bahrami/aa/picture alliance

Mata da 'yan mata sun fi wahala daga mummunan tasirin annobar corona, inda baya ga karancin kudin shiga, suka yi ta fuskantar cin zarafi irin dabam-dabam ciki har da fyade. Tuni ma kungiyoyi irin su Save the Children da ko kuma Asusun tallafa wa yara na duniya UNICEF suka nuna fargaba dangane da makomar ilimin yara mata a Afirka. Andile Dube, jami'ar da ke kula da ilimi a reshen UNICEF na Afirka ta Kudu ta tabbatar da mawuyacin halin da yaran mata ke ciki."A Afirka ta Kudu, kamar sauran kasashe da yawa da aka rufe makarantu a watan Maris, kusan yara miliyan 30 ba su samu damar yin karatu ba, imma ma su bin tsarin ilimi na gwamnati ko kuma masu bin tsarin ilimi mai zaman kansa. COVID-19 ya habaka rashin daidaiton da ke akwai, masu fama da talauci ba su da damar samun ilimin, yayin da yara masu galihu ke da yawancin dama." 

Karin Bayani: An dage shirin rigakafin COVID-19

Kididdigar da Hukumar ilimi da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta fitar ta nuna cewa kashi 8.3 % na daliban da suka yi rajista a duniya na ci gaba da zaman gida sakamakon rufe makarantu ko koyarwa daga nesa. Hasali ma dai daukacin makarantun kasashe bakwai na yankin Saharar Afirka suna rufe a halin yanzu. A bangaren kiwon lafiya kuwa, yaki da cututtukan da ke addbar Afirka kamar zazzabin cizon sauro da HIV / AIDS sun tsaya cik tun bayan bullar annobar Covid-19. Karin mutane 148,000 suka mutu sakamakon kamuwa da kwayar HIV a 'yan watannin baya-bayannan, saboda mutane kalilan ne aka yiwa gwajin cutar HIV/Aids tun lokacin da annobar corona ta barke. Fatan wasu 'yan Afirka na rabuwa da annobar ya karu bayan da aka gano allurar rigakafin corona. Amma kuma gwamnatocinsu ba su hanzarta odar alluran ba, lamarin da ke haifar da damuwa wajen tinkarar annobar a duniya baki daya, sai dai wasu kasashen nahiyar da suka fi karfin arziki irin su Afirka ta Kudu da Najeriya Fulani makiyaya cikin fargaba sun yi nasarar shigo da adadin da bai taka kara ya karya ba na allurar rigakafin covid-19.

Nijar: Matakan kariya a makarantu saboda corona

02:37

This browser does not support the video element.