1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Corona ta kama 'yan wasa a Afirka ta Kudu

August 20, 2020

Wasu 'yan wasan kwallon gora guda biyu na Afirka ta Kudu sun kamu da coronavirus. Hukumar da ke shirya wannan wasa a kasar ce ta tabbatar da haka a wannan Alhamis.

Lance Klusener wird neuer Cheftrainer des afghanischen Cricket-Nationalteams
Hoto: picture-alliance/empics/M. Ntombela

Bullar coronar dai a cikin 'yan wasan na kwallon gora  na zuwa ne a yayin da a jiya Alhamis aka bude wani wasan Cricket wurin shakatarwar da ake kira Kruger National Park. 

Hukumomin kasar ba su bayyana sunayen 'yan wasan da suka kamu da coronar ba, amma sun ce sun yi wa mutane 50 gwaji, a cikinsu ne kuma aka samu wadannan mutane biyu masu dauke da cutar. A halin da ake ciki dai an kebe masu cutar kuma likitoci na ci gaba da kula da su.