1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona ta yi ajalin tsohon firaministan Libya

April 5, 2020

Cutar Coronavirus ta yi sanadin mutuwar Tsohon Firaministan Libya Mahmoud Jibril.

Libyen Ministerpräsident Mahmud Dschibril in Tripolis
Hoto: dapd


Jibril mai shekaru 60 dai ya kamu da Corona a watan da ya gabata a kasar Masar inda yake da zama a 'yan shekarun baya-bayan nan.

Ya kasance mai fada-a-ji a gwamnatin Tsohon Shugaban Libya  Marigayi Muammar Gaddafi. Sai dai Jibril ya juya wa Gaddafi baya inda ya shiga cikin tawagar wadanda suka yaki Gaddafi har daga bisani ya zama Firaminista na wucin gadi bayan kifar da Shugaba Gaddafi. 

Sanarwa daga jam'iyyar Mahmoud Jibril da ke Libya ta ce tsohon firaministan ya mutu a wannan Lahadi a wani asibitin kudi da ke kasar Masar. Kawo wannan Lahadin dai mutum 18 aka tabbatar na dauke da cutar Coronavirus a Libya.