Diyya a sakamakon illar riga-kafin corona
February 22, 2021Biyan diyyar ya danganta ga wadanda aka yi wa allurar a karkashin shirin samar da magani na Covax. Lamarin da ake ganin ka iya kawar da shakku a tsakanin jama'a dama gwamnatoci a game da illolin da ake fargabar allurar rigakafin cutar mai kama numfashi na iya haifarwa.
A daya bangaren kuwa, wani bincike na masana da aka gudanar a Britaniya, ya nuna yadda aka samu raguwar yaduwar cutar corona saboda tasirin allurar rigakafin, wanda ke nufin zai matukar yin tasiri a sauran kasashen duniya, muddun aka rungumi tsarin yi wa al'umma allurar riga-kafin cutar.
A yankin Turai kuwa, gwamnatin kasar Italiya ta kara tsawaita dokar hana shige da fice a tsakanin kasar da sauran kasashe na yankin Turai. Sabuwar gwamnatin Firaiminista Mario Draghi, ta ce ta dauki matakin ne don shawo kan annobar corona da ke ci gaba da yaduwa a sassan kasar. Kasar ta ce za ta ci gaba da dokar kulle har ya zuwa ranar 27 ga watan Maris.