1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

An samar da kwayar maganin corona

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 23, 2021

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna da Amirka, ta amince a yi amfani da maganin corona da kamfanin Pfizer ya samar.

Coronavirus | Pfizer Covid Pille
Za a fara amfani da kwayar maganin Paxlovid a AmirkaHoto: Pfizer/REUTERS

Hukumar ta ce ana iya amfani da maganin mai suna Paxlovid ga marasa lafiyar da ke dauke da alamomin corona da ba su yi tsanani ba, domin kaucewa ta'azzarar cutar. Hukumar ta FDA ta nunar da cewa, Paxlovid ne maganin kwaya na farko na kwaya da aka amince a yi amfani da shi a Amirkan. Za dai a rinka bayar da maganin ne tare da umurnin likita, sai dai kuma za a bayar da shi kyauta. Gwamnatin Amirka ta yi odar fakiti miliyan 10 na kwayar maganin da kudinsa ya kama kimanin dalar Amirka biliyan biyar da miliyan 300.