Faransa da Italiya ce sun adadin mutuwar ya ragu
April 13, 2020Talla
A kasashen Italiya da Faransa da Amirka adadin wadanda suke mutuwar a kowace rana da cutar ta Coronavirus ya ja baya. Italiya ta ce a jiya Lahadi a cikin kusan mako uku an samu karancin wadanda suka mutu a rana guda da mutu 431
Domenico Arcuri, babban kwamishina ne na kiwon lafiya. Ya ce: ''har yanzu ba a ci karfin kwayoyin cutar ba, amma dai muna kan kyakyawar hanya a kullum muna samun kwarin giwa za mu yi nasarar samun bakin zaren.'' Kusan mutane dubu 20 suka rasa rayukansu a sanadin cutar ta Coronavirus a Italiya.