Coronavirus: Duniya na fuskantar karancin na'urar Ventilator
April 3, 2020A kasar Spaniya, sabbin alkaluma sun nunar da cewa, an sami karin wasu mutum kimanin 900 da cutar Coronavirus ta kashe a kwana guda, hakan na nufin annobar ta yi sanadiyar rayuka fiye da dubu goma tun bayan bullar ta a cikin kasar da ke yankin Turai.
Kasar Habasha na daya daga cikin kasashen Afirka masu tasowa da cutar Coronavirus ta bulla inda yanzu haka ake da mutum akalla 29 da aka tabbatar na dauke da cutar a cikin kasar, likitoci sun baiyana damuwa kan halin da za a iya fadawa ciki muddun ba a tanadi na'aurar taya numfashi da aka fi sani da Ventilator ba, cutar Covid-19 mai kama numfashi na jefa marasa lafiya cikin yanayi na bukatar na'urar, wanda yanzu haka kasar mai al'umma fiye da miliyan dari ke cewa tana da Ventilator hamsin da hudu kacal.
Baya ga kasar Habasha sauran kasashen Afirka ya zuwa na nahiyar Turai da Asiya, duk sun dukufa a aikin kera sabbin Ventilators, na'aurar mai matukar mahinmanci a wannan yanayi da ake ciki na yakar annobar Coronavirus.
A yankin Hong Kong kuwa, jama'a sun shiga rudani bayan umarnin gwamnati na hana fita har tsawon makonni biyu da gwamnatin yankin ta sanar a daren jiya Alhamis. Jama'a da dama sun koka kan rashin fayyace musu yadda dokar za ta yi aiki da kuma wadanda ta shafa. Tuni dai aka hana taron jama'a fiye da hudu da kuma rufe duk wuraren da ake sayar da barasa. Kawo yanzu mutum sama da dari takwas aka tabbatar sun kamu da cutar a Hong Kong, tuni hudu suka riga mu gidan gaskiya.
Yawan mutanen da cutar Covid-19 ta kashe a sassan duniya tun bayan bullarta a Disambar bara, sun haura miliyan daya kamar yadda alkaluma na jiya Alhamis suka nunar, cutar na ci gaba da yaduwa kamar wutar daji a Amirka a yayin da alkaluman mamata ke ci gaba da haurawa a kasar Spaniya.