Hajjin bana a cikin dokar nesa-nesa
July 6, 2020Talla
Hukumar takaita bazuwar cututtuka ta kasar Saudiyya ta ce babu batun taba dakin Ka'aba, kuma alhazai za su rinka barin tazarar akalla mita daya da rabi a tsakaninsu. Kazalika za a takaita mutanen da za su je filin Arfa da zuwa Muzdalifah, sannan wajibi ne alhaji da sauran jami'ai su kasance sanye da takunkumi a kowane lokaci.
Wadannan sabbin dokoki dai na zuwa ne bayan Saudiyya ta sanar da cewa mutum 1000 kawai ta amince su yi aikin hajjin. A kwanaki kuma Saudiyya ta ce ta dakatar da musulman kasashen duniya daga zuwa wannan ibada, duk dai a kokarin hana bazuwar coronavirus, wace ta addabi duniya.