Chaina: Raguwa da karuwar Coronavirus
February 17, 2020Talla
Baki daya dai mutane 1,800 ne suka rasa rayukanasu sakamakon wannan cuta da ke saurin yaduwa a Chainan, yayin da adadin mutanen da suka kamu da ita ya karu da sama da 2000, inda yawan masu dauke da cutar a yanzu haka ya kai dubu 70 da 500. Koda yake za a iya cewa a kwanakin baya-bayan nan adadin yaduwar cutar ya ragu, in banda a Lardin Hubei da ke zaman tushen Coronavirus din. Sai dai Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta yi gargadin cewa ba girin-girin ba dai ta yi mai.