Mutum guda ya mutu a kasar Philippines
February 2, 2020Talla
Wannan al'amari ya sanya jami'an kiwon lafiya a kasar ta Philippines gudanar da gwajin gaggawa a kan wata mace mai shekaru 38, wacce suka shigo kasar tare da mamacin daga Chaina, kuma tuni sakamakon gwajin ya tabbatar da tana dauke da kwayar cutar Coronavirus. Yanzu haka dai hukumar lafiyar kasar ta killace ta a babban asibitin birnin Manilla.
Wannan shi ne karo na farko da wani ya mutu a wajen kasar Chaina tun bayan billar cutar. Yanzu haka shi ma Shugaba Rodrigo Duterte na kasar ta Philippines ya bi sahun takwarorinsa na kasashen ketare wajen dakatar da tafiye-tafiye tsakanin al'umma da nufin hana cutar ta Coronavirus yaduwa.