1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani dan China ya mutu a Paris da ciwon Coronavirus

Abdourahamane Hassane
February 15, 2020

A karon farko an samu wani wanda ya kamu da cutar Coronavirus da ya mutu da ciwon a wajen Asiya a Faransa.

Frankreich Paris Eingang Bichat Krankenhaus
Hoto: picture-alliance/Photoshot/E. Laurent

Ministan kiwon lafiya na Faransa a wani taron manema labarai da ya kira ya ce wani dan yawan bude ido dan Kasar China da ke yIn jinyar cutar tun cikin wata Janairu ya mutu a wani asibiti da ke a Paris. Wannan shi ne karon fari da wani wanda ke fama da cutar ta Coronavirus ya mutu a nahiyar Turai. Ciwon na Coronavirus da ke shafar numfashi wanda aka gano a cikin watan Disanmba a lardin Hubei na China yanzu haka ya kashe mutane 1550 a Chaina kana wasu dubu 66 suka kamu da shi.