Jamus:Mutane da yawa na cikin hadarin kamuwa da Coronavirus
March 11, 2020Gwamnatin kasar Jamus ta ce akwai yiwuwar kashi saba'in cikin dari na al'ummar kasar su kamu da cutar nan ta Coronavirus a wata sanarwar da ke nuna munin cutar da ke ci gaba da bazuwa a sassan duniya. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel dai, ta nemi hadin kan jama'a don ganin an yi nasara kan cutar mai kama numfashi.
A birnin Madrid na kasar Spain kuwa, mutum goma cutar ta halaka a wannan Laraba a yayin da mutum fiye da dubu daya ke jinyar cutar a yanzu haka. A Afrika ta Kudu ta Kudu kuwa an gano wasu mutum kimanin shida da suka kamu da cutar, mutum akalla13 ne suka kamu da cutar a kasar.
Kasashe musanman na yankin Turai sun hana duk wani taro na jama'a da ya zarta mutum dubu daya tare da daukar matakan rufe kan iyakokinsu wasu kasashen kuwa sun bayar da umarnin rufe makarantu na tsawon makonni biyu. A kokarin da ake, na son ganin bayan annobar da ke son zame ma duniya alakakai. Tun bayan bullar cutar a Chaina a Disambar bara, ta halaka mutum fiye da dubu hudu ta kuma yadu zuwa kasashen duniya fiye da dari.