1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Coronavirus na ci gaba da kisa a China

January 23, 2020

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce tana tattara bayanai daga masana kan sabuwar cutar Coronavirus mai kisa cikin gaggawa da a yanzu ke barna a China bayan shiga kasar Amirka da ta yi.

China Coronavirus
Hoto: picture-alliance/Xinhua/X. Yijiu

Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta dakatar da matakin da ta so dauka, na bayyana sabuwar kwayar cutar nan ta Coronavirus da ta bulla a China, a matsayin wata barazana ga duniya.

A wata ganawar gaggawa da ta yi da kwararru, hukumar ta ce za a saurarin karin wasu hujjojin da za su tabbatar da kasancewar cutar a matsayin babban bala'i da ke bukatar mataki na gaggawa, kafin a kai ga tabbatar da ita a matsayin.

Wannan cuta ta Coronavirus dai tuni ta bazu a China inda ta kama mutum 444, 17 kuwa suka mutu. Haka nan ma cutar ta shiga kasar Amirka 

Tuni dai hukumomin yankin da ta bulla a ciki wato birnin Wuhan, suka hana shiga da fitar jama'a, musamman ma zirga-zirgar jirage.