Coronavirus na karuwa a Najeriya
March 22, 2020A Najeriya alkaluman wadanda suka kamu ya karu, inda a yanzu ake da mutum 27; kuma jihar Legas ce ke kan gaba da mutum 19, Abuja na da hudu, Ogun mutum biyu, yayin da jihohin Ekiti da Oyo ke da guda-guda.
Ko a Jamhuriyar Nijar ma an sami karin mutum guda da ya kamu, bayan na farko da hukumomi suka tabbatar.
Tuni ma Ruwanda, ta kafa dokar hana zirga-zirga a fadinta tare da rufe dukkanin iyakoki, a tsayuwar da ta yi kan yaki da cutar cutar COVID-19 da ke ci gaba da tayar da hankalin duniya a yanzu.
Ruwandar dai ita ce kasar farko a Afirka da ta dauki wannan mataki mai tsauri, yayin da duniya ke nuna fargabar yadda matsalar ke iya kasancewa lokacin da ta soma bazuwa a nahiyar.
Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, ta nuna damuwa da yanayin rashin ingancin cibiyoyin lafiya da za su iya kula da mutane a kasashen na Afirka.