1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

COVID-19: Za a bude ma'aikatun Najeriya

April 30, 2020

A wani abun da ke zaman kokari na kaucewa shiga tsaka a cikin wahala, gwamnatin Tarayyar Najeriya ta nemi bankuna da sauran kamfanoni da ma ma'aikata da su koma bakin aiki daga Litinin din makon gobe.

Nigeria - Western Union Zweigstelle in Benin
Ma'aikatan gwamnati za su koma bakin aiki a NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

Duk da cewar dai Tarayyar Najeriyar na dada nisa a cikin annobar COVID-19, daga dukkan alamu kuma batu na tattalin arzikin kasar na kara daukar hankalin mahukunta da ke  neman rage radadi na rashin da 'yan kasar suke fuskanta yanzu.Tuni dai gwamnatin ta dauki jerin matakan bude tattalin arzikin, da suke shirin fara aiki daga Litinin din mako mai zuwa.

Bude ma'aikatu da kamfanoni

A cikin jerin farko dai kuma a bisa umarni na shugaban kasa, ma'aikatan gwamnati na shirin sake komawa bakin aiki, a yayin da kamfanonin da ke da ruwa da tsaki da abinci da magani, suma suka samu izinin budewa. Ko bayan nan dai Najeriyar ta kuma yarjewa kamfanonin da ke aikin manyan hanyoyi komawa bakin aikin.

Kamfanoni za su koma aikiHoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Ya zuwa yanzu dai, an fara aikin feshi ga wasu jiragen saman kasar, a wani abin da ke zaman mataki na gaba na ingantar zirga-zirga a tsakanin sassan Najeriyar da ke da tasiri ga rayuwar al'umma. Bashir Ahmed guda ne cikin masu bai wa shugaban kasar shawara, kuma a fadarsa tunanin rage radadin ne ya kai ga shugaban kasar yanke hukuncin dage takunkumin a wasu bangarorin tattalin arziki, ba tare da yin illa ga lafiyar al'umma ba.

Duk da cewar dai Najeriyar na fuskantar karuwa cikin yaduwar cutar,  karuwar talauci na kara tayar da hankalin 'yan mulki,nda a wasu jihohin suka kalli wasoso na abinci, a wani abin da ke zaman ba sabun ba. Kuma ko bayan nan da akwai fatan sake bayar da damar yin aikin, ka iya taimakawa ita kanta gwamnatin da ke matukar bukatar kudi domin sauke nauyin da ke ta kara karuwa a halin yanzu.

Najeriya cikin rashin kudiHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Lawal Habib dai na zaman wani masani na tattalin arzikin kasar da kuma yake kallon sabo na matakin a matsayin mai riba, kama ga ita kanta gwamnatin ya zuwa al'ummar kasar da ke shirin biyan haraji bayan rushewar man fetur da kasar ta dauki lokaci tana dogaro da shi a fannin kudin shiga.

Matakan rage kashe kudi

Abujar dai na fatan samun bashin Naira miliyan dubu 850 daga kasuwannin kudin cikin gidan da su kansu a yanzu, ke fatan sake farfadowar harkokin ka iya kai wa ga matsar mai daga dutse. A nata bangaren, gwamnatin ta fara shirin rage ma'aikatu da hukumominta, a wani mataki na rage kisan kudin da ake da bukata domin ingantar rayuwar 'yan kasar da ke halin babu a yanzu. An dai dade ana ta korafi na fadin da gwamnatin ke da shi, abin kuma da ke lashe da dama cikin kudin kasar ba tare da tasirin da ake fatan gani tsakanin al'umma ba.