1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar EU ta yi alkawarin tallafawa kasashe matalauta

Ramatu Garba Baba
April 7, 2020

Likitan Najeriya na daga cikin dubban dubatan da cutar Coronavirus ta halaka a sassan duniya, a yayin da gwamnatoci ke ci gaba da daukar matakai don ganin an dakile annobar da ta karadde duniya.

TIB Molbiol - Coronavirus Test
Hoto: picture-alliance/Kitty Kleist-Heinrich/Tagesspiegel

A Amirka, mutum fiye da dubu daya ne suka mutu a wannan rana ta Talata a sakamakon cutar Coronavirus, gwamnan New York Andrew Cuomo ya ce, alkaluman mamata a sanadiyar cutar mai kama numfashi a jihar, ya zarta adadin wadanda suka mutu a yayin harin ta'addanci na ranar sha daya ga watan Satumba a kasar. Britaniya na biye wa Amirka a yawan mamata daga annobar, na yau Talata, a daidai lokacin da hankulan al'ummar kasar suka karkata kan tsananin rashin lafiyan Firaiministan kasar Boris Johnson da yanzu haka ke kwance a asbiti inda likitoci ke ba shi kulawa ta musanman.

A Najeriya, inda masana ke baiyana damuwa kan halin ko-in kula da jama'a ke nunawa a yaki da ake da cutar ta Covid-19, gwamnatin jihar Katsina da ke arewacin kasar, ta sanar da mutuwar wani likita mai suna Dakta Aliyu Yakubu mazaunin garin Daura, bincike ne ya tabbatar, cutar ce ta kashe likitan da ke da wani asibiti mai zaman kansa a jihar kamar yadda gwamnan Aminu bello Masari ya tabbatar a dazun nan a wani taron manema labarai

Kungiyar tarayyar Turai ta EU, ta ce ta ware kimanin yuro biliyan goma sha biyar, don tallafawa kasashe matalauta don su yaki annobar Coronavirus, Shugabar hukumar zartsawa ta EUn, Ursula von der Leyen, ta ce kudadden zasu taimaka wajen inganta fannin lafiya da tattalin arzikin wadannan kasashen da tuni ya kara tabarbarewa a sakamakon wannan annobar. 

Matakan hana yaduwar cutar a nahiyar Turai kadai ba zata iya yin tasiri ba, inji kungiyar, muddun aka bari cutar ta ci gaba da yaduwa a sauran sassan duniya. Ba a dai kai ga baiyana sunayen kasashen da zasu ci gajiyar kudadden ba tukun na, amma mambobin kungiyar na ganin nahiyar Afrika ce sahun gaba saboda dangantakarta da Turai da kuma rashin ingancin tsarin lafiyar kasashen yankin. A gobe Laraba za a kamalla tattaunawar kan yadda za a raba wadannan kudadden ga kasashe mabukata.

A nan Jamus kuwa, masu shigar da kara sun ce, sama da yuro miliyan goma sha hudu da aka ware don siyan kyallayen rufa fuska ne suka fada hannun 'yan damfara. An bayar da odar tun a watan Maris din da ya gabata, a yayin karbo kayayyakin ne aka gane akwai lauje cikin nadi. Jamus na ci gaba da daukar matakan yakar cutar da tuni ta lakume dubban rayuka.