Kalubalen da Italiya ke fuskanta a yaki da Coronavirus
February 25, 2020Italiya ta kasance kasar Turai da ta fi kowacce yawan mutanen da suka kamu da kwayar cutar Coronavirus da yawansu ya kai 322 daura da wasu goma da suka mutu. Yanzu haka mahukuntan kasar sun dauki tsaurara matakai don dakile yaduwarta ta hanyar killace dubban dubatan mutane a yankin arewacin Italiya. Akwai kalubale da mahukunta suka fuskanta na karin farashin man nan na kashe kwayoyin cuta da kuma jami'an agaji na bogi da ke ikirarin 'yan kungiyar Red Cross ne, da aka gano a yayin da ake kokarin shawo kan annobar.
An girke jami'an 'yan sanda gudu biyu, wadanda ke dakatar da motocin da ke kokarin bin sha tale-talen da ke shiga yankin da aka killace a arewacin kasar ta Italiya, yankin da cutar ta Coronavirus ta fi kamari inda ´kuma tuni aka haramta shige da ficen wannan gari da ke da mutane kimanin dubu hamsin.
Matakin killace wannan gari dai na bangaren yunkurin gwamnati na kaucewa yaduwar cutar zuwa wasu yankuna. Jami'an 'yan sandan na bin motocin da suka yi jerin gwano daya bayan daya ana karkatar dasu daga shiga yankin da akasawa suna "red zone". Wani direban babbar mota na tsaye na a gefen hanya. Shi dai ba dan wannan yanki ba ne, amma ya hakikance cewar wannan haramtacciyar hanyar ce kadai zai iya bi.
Ana iya ganin jerin gwanon motoci akan hanyoyin, wadanda jami'an 'yan sandan ke bincike, wasu direbobin na dauke da takardun izini na musamman. A yayin da wasu ke kokarin nunar da cewar za su iya cigaba da bin wannan hanya. Mitoci kadan daga inda 'yan sandan suke, akwai wasu maza guda biyu suna tsaye. Sunan daya daga cikinsu Vinicio wanda ke daure da takunkumin baki, kuma yana zama ne a garin Casalpustelengo. Kamar yadda ake hana motoci shiga yankin, su ma wadanda ke ciki haka aka hanasu fita, sai dai magana daga nesa."Vinicio ya ce ba mu da izinin shige wannan layin da aka zana. Don haka muna jiran abokan aikinmu da ke yankin da ba a killace ba, su kawo mana na'urar komfuta domin muyi aiki dasu daga gida" Da farko dai abun ya dan tayar wa da jama'a hankali, kafin lamarin ya fara zama jiki a cewar mazauna wannan yanki. Wajibi ne a cigaba da killace yankin arewacin Italiyan na tsawon makonni biyu. Mutane kamar su Vinicio basa iya fita daga gidajensu sai dai idan ya zama dole. Kowa na fatan ganin wucewar kwanakin killacewar, domin rayuwarsu ta koma kamar da.