Bukukuwan Krismeti na 2021
December 23, 2021Talla
Mabiya addinin kirista a duniya na shirin gudanar da bubukuwan sallah Kirismeti cikin yanayi na taka-tsantsan a sakamakon annobar cutar corona da ta yi wa duniya dabaibayi.
A wasu kasashen duniya kamar nahiyar Afirka, jama'a na cike da fargaba a sakamakon matsalolin tsaro dama barazanar ta annobar corona da suka haifar da tsaiko, a daidai lokacin da Kristoci ke bikin tuni da ranar haihuwar Yesu Almasihu.