COVID-19: Zaman gida a duka jihohin Najeriya
April 23, 2020Ya zuwa yanzu dai annobar ta COVID-19 ta isa zuwa jihohi 25 da Abuja, a wani abu da ke kara tayar da hankali sannan kuma yake nuna irin jan aikin da ke gaban 'yan mulki na kasar. Jihohin kasar sun bi sahun tarayyar wajen haramta zirga-zirga a tsakaninsu ne, biyo bayan rahotannin da ke nuna cewa annobar na yaduwa ne sakamakon tasiri na zirga-zirgar.
Taron samo mafita
Bayan kammala wani taro da suka gudanar ta kafofin sadarwa na zamani dai, gwamnonin sun ce daga yanzu har zuwa tsawon makonni biyun da ke tafe, an haramta zirga-zirga a tsakanin wata jihar zuwa wata da nufin kaucewa kara yaduwar cutar mai tayar da hankali.
Abdulrazak Bello Barkindo dai na zaman kakakin kungiyar gwamnoni ta kasar, da kuma ya ce zirga-zirgar ta kara ta'azzara yaduwar cutar a tsakanin sassan Tarayyar Najeriyar.
Fafe gora ranar tafiya
To sai dai koma wane irin tasiri kaurar da ta kunshi 'yan boko da ma talakawa ke iya yi a kan karin yaduwar annobar ta COVID-19 dai, akwai alamun makara ga jihohin da suka kalli tururuwa ta mutane daga manyan biranen Legas da Abuja ya zuwa garururuwansu na asali da nufin kaucewa annobar. Dr Umar Tanko na zaman kwararre akan kula da lafiya a matakin farko, da kuma ya ce akwai bukatar kara dakatar da kai kawon har a cikin jihohin, domin tabbatar da hana yaduwar cutar daga wani yankin na jiha zuwa wani.
In har likitoci suna tunani na lafiyar al'umma, ga masu kwadagon Tarayyar Najeriya da ke kirga asarar aiki sakamakon matakin killace al'ummar dai, wai abin da lafiyar take shiri ta bukata na zaman na kan gaba akan hanyar warware matsalar. Kuma tuni kungiyar kwadagon kasar ta aike da wasikar neman kaucewa kara tsawon wa'adin zaunawa cikin gidan ga gwamnatin tarayya. Comrade Kabir Nasir dai na zaman sakataren tsare-tsare na kungiyar kwadagon kasar ta ULC, da kuma ya ce matakin gwamnonin ba shi shirin tasiri ga kasar da batun yunwar ke gaban COVID-19 wajen barna. Tuni dai wasu a cikin jihohi na kasar suka fara batun rage albashin ma'aikata da nufin tunkarar tasirin annobar da ke barazanar rushe kudin shiga na jihohin ko bayan faduwar farashin man fetur a duniya.