Zaman taron tattalin arziki kan annobar Coronavirus
March 3, 2020A yayin da a karon farko aka sami bullar cutar Coronavirus a kasar Ukraine da ke gabashin Turai, ita kuwa gwamnatin kasar Faransa ce ta bayar da umarnin rufe makarantu kimanin dari biyu da ashirin bisa fargabar da ake ciki, na ci gaba da yaduwar cutar.
A kasar Iran kuwa, wani babban jami'i a hukumar bayar da agajin gaggawa ne ya kamu da cutar mai kama numfashi, yana daya daga cikin manyan jami'an gwamnati da cutar ta Covid-19 ta kama, da safiyar wannan Talatar jagoran addini, Ayatollah Ali Khamenei ya nemi taimakon rundunar sojin kasar, don yakar cutar da ta riga ta halaka mutum kimanin ashirin da tara a Iran.
A wani lokaci a wannan Talata, ministocin kasashen duniya bakwai masu karfin tattalin arziki za su yi wani zama na musanman don tattauna batun Coronavirus, ganin yadda ta ke barazana ga tattalin arzikin duniya. Mutum sama da dubu uku cutar ta kashe tun bayan bullarta a Disambar bara, akasarinsu a kasar Chaina.