1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

COVID-19: Najeriya ta cire kudin lantarki

Uwais Abubakar Idris LMJ
April 9, 2020

A ci gaba da daukan matakai na saukakawa al'ummar Najeriya daga matsin rayuwa sakamakon cutar Coronavirus a kasar, kamfanonin samar da hasken wutar lantarki sun amince da bayar da wutar lantarkin ta watanni biyu kyauta.

Afrika Elektrizität Nigeria Afam VI
'Yan Najeriya za su samu hasken wutar lantarki kyautaHoto: Getty Images/AFP/F. Plaucheur

Wannan mataki dai ana kallonsa a matsayin gudummawa daga fannin kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki a Najeriyar, domin saukakawa 'yan Najeriyar halin da suka shiga na koma bayan tattalin arziki, saboda dokar kowa ya zauna a gida domin dakile yaduwar cutar ta Coronavirus, abin da ya durkusar da tattalin arzikin mutane da dama musamman masu karamin karfi.

Hasken wutar lantarki yayin zaman gida

A sanarwar da Sunday Oduntan daraktan gudanarwa kuma mai Magana da yawun kamfanonin ya sanyawa hannu, ya ce wannan kari ne daga tabbaci na samar da wutar lantarki ga 'yan Najeriyar a lokacin wannan matsi na Coronavirus.

Hasken wutar lantarki na karanci a NajeriyaHoto: picture-alliance/dpa/A. Jallanzo

Sakacin likitoci

A yayin da ake wannan hali ana nuna damuwa a kan yanayin da wasu likitoci ke nunawa na sakaci a game da yaki da cutar ta Coronavirus, musamman abin da ya faru a jihar Kwara, inda wani likita Farfesa ya ki bayyana cewa mara lafiya da ya kai asibitin birnin Ilorin na da cutar Coronavirus har sai bayan mutuwarsa, abin da ya jefa mutane da dama cikin hatsari, domin sama da mutane 60 aka kebe a kan haka. 

Ministan shari'a  na Najeriyar Abubakar Malami ya ce akwai doka a kan masu irin wannan sakaci. A yayin da Najeriyar ke ci gaba da yaki da cutar ta Coronavirus, kwararru na bayyana bukatar kara taka tsan-tsan a kan lamarin, inda gwamnatin ta sanar da zabtare kasafin kudin wannan shekara da kaso 20 cikin 100.