1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a iya samun karancin magunguna a nahiyar Turai

Binta Aliyu Zurmi
February 13, 2020

Ministan kiwon lafiyar Jamus Jens Spahn ya ce bullar cutar Coronavirus a China za ta iya kawo karancin magunguna a nahiyar Turai, saboda galibin sinadarai da ake amfani da su wajen hada magununa na fitowa ne daga China.

Gesundheitsminister Jens Spahn CDU
Hoto: Reuters/M. Tantussi

A wani taro da ministocin kiwon lafiya na kasashen da ke cikin Kungiyar EU a birnin Brussels na kasar Beljiyam, ministan na lafiya na Jamus ya ce ya kyautu EU din ta nazari kan wannan batu don samo mafita cikin hanzari. 

Ministan Spahn har wa yau ya ce akwai bukatar samun hadin kai da kuma fidda hanyoyi na tantance cutar tsakanin kasashen kungiyar don dakile yaduwar cutar.