1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin tabbas a zaben Cote d'ivoire

Abdoulaye Mamane Amadou LMJ
October 19, 2020

A yayin da ake ci gaba da yakin neman zaben shugaban kasa a kasar Cote d'ivoire, har yanzu da akwai rashin tabbas kan yadda zaben na ranar 31 ga wannan wata na Oktoba zai wakana.

Elfenbeinküste Wahlen Alassane Ouattara
Alassane Ouattara shugaban kasar Cote d'ivoire da ke son yin tazarce Hoto: Yvan Sonh/Xinhua/picture-alliance

Yayin da 'yan adawar kasara ta Cote d'ivoire suka yi kira ga magoya bayansu su hana gudanar da zabe a kasar dai, a hannu guda bangaren gwamnati sun bayyana cewa hakan ya sabawa tafarkin dimukuradiyya. Magoya bayan jam'iyyar RHDP da ke mulkin kasar Cote d'Ivoire dai, sun yi gangamin nuna goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa kana shugaba mai ci a kasar Allassane Ouattara yayin da yake kaddamar da gangamin yakin neman zaben tazarecensa a wa'adin mulki karo na uku, a yankin Bouake da ke zaman tsohuwar cibiyar 'yan tawaye kuma birni na biyu mafi girma a yankin tsakiyar kasar.

 Karin Bayani: RHDP na neman Ouattara ya tsaya takara

Duk da yake zaben na tattare da sarkakiya, Shugaba Ouattara bai yi kasa a gwiwa ba wajen bayyyana cewa shi ne ke da yawan magoya baya, a daidai lokacin da 'yan adawa ke ci gaba da yin matsin lamba kan yunkurinsa na neman sake lashe zabe.
Sai dai a yayin da a hannun guda shugaban kasar mai shekaru 76 ke neman karin wa'adin mulkin kasar da ke zaman mafi karfin tattalin arziki a kasashen yankin yammacin Afirka renon Faransa ke ta yakin neman zabe, a nasu bangare 'yan adawa kira suka yi da a juyawa zaben baya, hasali ma a yayin wani taron manema labarai da suka jagoranta, Pascal Affi N'Guessan da Henri Konan Bédié sun yi kira ga magoya bayansu da su toshe duk wata hanya ta gudanaar da zaben, kamar yadda dokokin kasar suka tanada.

Jagororin adawar Cote d'ivoire Pascal Affi N'Guessan da Henri Konan BédiéHoto: Sia Kambou/AFP/Getty Images

Karin Bayani: Bore kan fasarar kundin tsarin mulki a Cote d'ivoire

Wannan kiran da 'yan adawar kasar suka yi ya kara jefa shakku a zukatan al'umma kwanaki bayan kaddamar da yakin neman zaben, hakan kuma hukumomin kasasa da kamar Tarayyar Afirka AU da ECOWAS da ma Majalisar Dinkin Duniya, sun aika wata tawagar gawana da bangarorin siyasar kasar domin cimma masalahala, batun kuma da kawo yanzu ya kasa tabuka komai a zaben. A shekarar 2010 zuwa 2011 dai wani rikicin siyasa ya hallaka daruruwan mutane a kasar bayan ya rabata gida biyu, rikicin da kuma ake fargabar sake samun irinsa a zaben na wannan shekara.