1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Covid-10: Saliyo ta sanya dokar hana fita

Ahmed Salisu
April 2, 2020

Hukumomi a kasar Saliyo sun sanya doka ta hana fita ta tsawon kwanaki uku a wani mataki na dakile bazuwa cutar nan ta Coronavirus wadda ta bulla a kasar har ma mutane biyu ya zuwa yanzu suka kamu da ita.

Coronavirus Symbolbild
Hoto: Reuters/D. Ruvic

Ministan tsaron kasar kana jami'in da ke kula da kwamitin da ke yaki da cutar ta Covid-19 a Saliyo din Kellie Conteh ne ya ambata hakan a jiya Laraba, kuma ya ce dokar ta hana fita za ta fara aiki ne daga ranar Lahadin da ke tafe.

A cewar ministan, hukumomi za su raba kayan aiki wadanda suka hada da kyallen rufe fuska da sauran kaya na kare kai daga kamuwa da cutar ga jami'an kiwon lafiya kasar sannan ya yi kira ga 'yan kasar da su dauki matakai na kariya daga cutar ta Covid-19.

'Yan Saliyo din dai na nuna fargaba game da yadda za a tinkari wannan annoba kasancewar kasar na kalubale babba a fanninta na kiwon lafiya.