1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona na bunkasa a Afirka ta Kudu

August 2, 2020

Ministan Lafiya na Afirka ta Kudu Zweli Mkhize ya ce kawo karshen makon nan kasar ta samu mutum sama da 500,000 masu coronavirus.

Südafrika Coronavirus Polizei schließt Barbershop
Hoto: Reuters/S. Hisham

A cikin wannan adadin mutum 8,150 cutar ta yi ajalinsu. Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa a kan wannan labari, tana mai gargadin cewa annobar za ta iya rayuwa na wani lokaci mai tsawo, abin da kuma ka iya sanyaya wa mutane gwiwa, kowa yaji ya gaji da ci gaba da yakarta. 

Sai dai duk da cewa akwai mutum fiye da rabin miliyan daya da suka kamu da cutar a Afirka ta Kudun, Shugaba Cyril Ramaphosa ya ce idan aka kwatanta da sauran kasashen duniya cutar ba ta yi kisa sosai a kasar ba, yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace.