1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin kasashe sun halarci taro kan cutar COVID-19

Zulaiha Abubakar
May 4, 2020

Shugabannin kasashe hadin gwiwa da kungiyoyi da kuma bankuna sun bukaci kudaden da yawansu ya kai dala biliyan takwas domin gano rigakafin cutar Coronavirus.

Symbolbild Corona-Virus Impfstoff
Hoto: picture-alliance/dpa/Geisler-Fotopress

An gabatar da wannan bukata ne yayin babban taron da ya gudana ta bidiyo a wannan Litinin din, wanda kungiyar EU ta shirya. a lokacin wannan taro dai babu wakilcin kasashen Amirka da Rasha duk kuwa da cewar annobar ta Covid-19 tayi sanadiyyar mutuwar mutanen da yawansu ya kai 67,000 a Amirka .

Da yake jawabi a lokacin taron babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya jaddada muhimmancin hadin kai da bukatar yin watsi da gasa a wannan lokaci na laluben rigakafin COVID-19, bayan ya jaddada bukatar amfani da kudaden a bangaren samar da rigakafin da kuma gudanar da sabbin gwaje-gwaje.