1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Coronavirus ta shafi masu cutar AIDs

Muhammad Bello LMJ
July 6, 2020

Annobar cutar coronavirus, ta haifar da mummnan tasiri ga yadda hukumomi da gwamnatocin duniya ke kulawa da ma su dauke da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV/AIDs ko kuma SIDA.

Indien Welt Aids Tag Ballon
Coronavirus na kawo nakasu ga kokarin yaki da cutar HIV/AIDs ko kuma SIDAHoto: picture-alliance/Pacific Press/S. Paul

A Litinin din nan ne dai aka bude taron makon yaki da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV/AIDs ko kuma SIDA da aka saba gudanarwa duk shekara. Taron na bana dai, na zuwa ne a daidai lokacin da duniya ke fama da matsalar annobar cutar coronavirus. Shekaru sama da 30 ke nan da bulla tare da yaduwar cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV/AIDs ko kuma SIDA a fadin duniya, kuma cutar ta ci gaba da yin mummunan tasiri. Ya zuwa yanzu Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta tabbatar cutar ta halaka sama da mutane miliyan 25, kuma kaso tara cikin 100 na wadanda suka rasa rayukansu 'yan Najeriya ne. Cikin haka ne kuma kwatsam aka samu bullar annobar coronavirus, wadda da alamu bullar ta ya haifar da nakasu a dukkanin kokarin da ake ga masu dauke da cutar ta HIV/AIDs din ko kuma SIDA da kuma ma kare yada ta.

Tsintar kai a cikin tasku

Madam Juliet Ejembo wata ce da ke dauke da cutar ta HIV/AIDs ko kuma SIDA, kuma ta ce a da suna samun kyakkyawar kulawa amma a yanzu lamarin ya sauya sakamakon bullar annobar ta COVID-19 kuma a yanzu nema take ta sare da rayuwar gaba daya. Dakta Lawson Kenneth likita ne da ke aikin duba ma su dauke da cutar ta HIV cewa ya yi: "Bullar cutar COVID-19 ta yi mummunan tasiri ga daukacin rayuwar jama'a da ma harkokin kula da lafiyarsu, ma su dauke da cutar HIV na ganin tasku, a gaskiya ba sa samun cikakkiyar kulawa kamar da. Kuma ga yadda likitoci irinmu ke kamuwa da cutar ta HIV dalilin mu'amala da ma su ita ya haifar da rage adadin likitoci a bakin aiki, baya ga karancin kayayyakin aiki na kare kai."
Madam Fortune Kalio ita ce shugabar kungiyar matasa masu dauke da cutar ta HIV/AIDs ko kuma SIDA, Association Of Positive Youths Living With HIV and AIDs a Najeriya: Sakamakon dokar zaman gida a dalilin annobar COVID-19, ma su dauke da cutar ta HIV da dama ba sa iya fitowa domin zuwa karbar magungunan da suka saba sha. Ko da sun iya fitowa asibitoci da inda suka saba karbar magungunan yawanci kulle suke. Sannan yanzu ba ma iya matsowa kusa da su saboda ka'idar bayar da tazara, hakan ya sa ba a iya aiwatar da wasu gwaje-.gwaje da aka saba yi a baya. Magungunan ma yanzu sun ja baya, sannan ganin raunin jikinsu, su kansu suna tsoron zuwa asibitoci. Da dama sun rame wasunsu sun rasa ayyukan yi, wasu da ke kasuwanci ya tsaya, mafi yawa yanzu a cikin halin tasku suke sosai.

Karancin magunguna da kulawaHoto: AP

Halin rashin tabbas

Bisa la'akari da yadda gwamnatocin tarayya da na jihohi a Najeriya suka karkata hankula kusan kacokan kan tunkarar annobar COVID-19 a halin yanzu, gami kuma da yadda tallafin kungiyoyi da hukumomi na kasa da kasa kan cutar ta HIV/AIDs ko kuma SIDA ke matikar raguwa, masu dauke da cutar da ma sababbin da za su kamu, na cikin halin rashin sanin tudun dafawa.