1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

COVID-19: Jamus ta bukaci hadin kan duniya

April 11, 2020

Shugaban kasar Jamus, Frank-Walter Steinmeier, ya bayyana halin da ake ciki na annobar coronavirus da wata jarrabawa ce ga karfin imanin bani Adama da wanzuwarsa.

Deutschland Berlin | Coronavirus | Frank-Walter Steinmeier, Bundespräsident
Hoto: Getty Images/Bundesregierung

Shugaban na Jmaus, Frank-Walter Steinmeier,na fadin hakan ne a jawabinsa na farko a hukumance bayan wanda ya yi lokacin Kirsimeti, inda ya jaddada bukatar taimakekeniya tsakanin jama'a.

Ya yi bayanin cewa Jamus ba za ta iya fita daga kangin wannan annoba ba, har sai ta taimaka wa makwabtanta da ke cikin ja'ibar cutar, a saboda hakan ne ya nuna muhimmancin hadin kai a tsakanin kasashen duniya.

Da yake martani kan wadanda ke cewa duniya na yanayi na yaki kuwa, Steinmeier, ya musanta hakan, inda ya ce babu kasar da ke fito-na-fito da wata a wannan lamarin, kawai dai gwaji ne ga imaninmu.